logo

HAUSA

Ya dace kasashen yamma su gane cewa “abun da ka shuka shi za ka girba”

2022-03-17 19:52:32 CRI

Gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake kasar Sin ta kira taron manema labarai a yau Alhamis, inda kakakinta Xu Guixiang ya ce, a halin yanzu ana gudanar da taro na 49 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva, inda akwai wasu kasashen dake kokarin jirkita gaskiya, da neman fakewa da batun kare hakkin bil-Adama a Xinjiang don su shafawa kasar Sin bakin fenti.

Xu ya ce, mutuntawa gami da kare hakkin dan Adam, ba maganar fatar baki ba ce, mataki ne na zahiri. Tun bayan da aka kafa Jamhuriya Jama’ar Kasar Sin a shekara ta 1949, ya zuwa yanzu, an samu ci gaba sosai a bangaren kare hakkokin dan Adam a jihar Xinjiang, baya ga dimbin nasarori da aka cimma a wannan fanni. Muna jan kunnen kasashen yamma cewa, akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a Xinjiang, don haka bai kamata su rika neman rura wutar rikici ba.

Xu ya kuma ruwaito wani karin magana na kabilar Uygur dake cewa, idan ka jefa dutse a sama, zai fada a kanka, wato abun da ka shuka, shi za ka girba, in ji malam Bahaushe. (Murtala Zhang)