logo

HAUSA

Ukraine ta hade turakun lantarkin ta da babban tsarin samar da makamashi na nahiyar Turai

2022-03-17 11:39:34 CMG

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce, kasarsa ta hade turakun lantarkin ta da babban tsarin samar da makamashi na nahiyar Turai.

Volodymyr Zelensky, wanda ya wallafa hakan a shafin tweeter, ya ce Ukraine ta zama mambar kungiyar samar da makamashi ta Tarrayar Turai. Yana mai cewa an kammala hade tsarukan makamashin Ukraine da na Tarayyar Turai.

A bara ne Ukraine dake samun wani bangare na wutar lantarkinta daga Rasha da Belarus, ta sanya burin hade tsarin makamashinta da na Tarayyar Turai, zuwa shekarar 2023.

Wasu rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, cibiyoyin nukiliya 15 na tashoshin makamashin nukiliya na Ukraine na samar da kimanin kaso 55 na bukatun lantarkin kasar. Tashohin lantarki masu amfani da tururi kuma na samar da kaso 29 na lantarkin, yayin da take samun abun da ya rage daga wasu hanyoyi ko kuma kasashen waje. (Fa’iza Mustapha)