logo

HAUSA

Sin: Makullin warware rikicin Ukraine yana hannun Amurka da NATO

2022-03-17 19:49:44 CRI

Dangane da zargin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi a baya-bayan nan cewa, wai kasar Sin ba ta yi Allah-wadai da matakin soja da Rasha ta dauka ba. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Zhao Lijian, ya bayyana Alhamis din nan cewa, kalaman da bangaren Amurka ya yi kan kasar Sin kazafi ne, kuma hakan ya kara fallasa ra'ayin bangaren Amurka na yakin cacar baka da yin fito na fito. Kuma irin wadannan kalamai ba za su taimaka wajen magance matsalar ba, kuma Sin na adawa da su matuka .

Zhao Lijian ya ce, matakin da gwamnatin Amurka ta dauka kan fadada kungiyar tsaro na NATO zuwa yankin gabashi, yana da alaka kai tsaye da rikicin dake faruwa a halin yanzu a kasar Ukraine. Ya ce, “Ita ma tsohuwa ‘yar majalisar dokokin Amurka Tulsi Gabbard ta bayyana cewa, muddin Amurka ta yi alkawarin ba za ta shigar da kasar Ukraine cikin kungiyar NATO ba, to za ta iya kawo karshen rikicin da kuma hana barkewar yaki, amma gwamnatin Amurka ba za ta yi hakan ba. Makullin warware rikicin Ukraine na hannun Amurka da NATO. Don haka, ina fatan Amurka da NATO, a matsayinsu na masu tayar da rikicin, za su yi tunani a kan rawar da suke takawa a rikicin na Ukraine, su dauki nauyin da ya dace, gami da matakai na zahiri don sassauta lamarin, da ma kawo karshen rikicin kasar Ukraine nan da nan."