logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci sassan Libyan da su rungumi jigon zaman lafiya

2022-03-17 10:41:39 CRI

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki a siyasar Libya, da su rungumi matakan da za su wanzar da zaman lafiya, tare da kaucewa duk abun da za su iya kara rura wutar tashin hankali a kasar.

Dai Bing ya ce baya ga al’ummun Libya, ragowar sassan kasa da kasa ma na fatan ganin kasar ta hau turba ta gari, ta ci gaba da samun bunkasa, tare da cimma zaman lafiya mai dorewa cikin sauri.

Jami’in ya kara da cewa, Sin ta gabatarwa masu ruwa da tsaki a siyasar Libya, shawarar kai zuciya nesa, a wannan lokaci mai muhimmanci. Kaza lika Sin na fatan za a ci gaba da aiwatar da matakan siyasa, kuma za su kaucewa daukar matakai da ka iya kara yamutsa yanayin da ake ciki.

Ya ce kamata ya yi sassan su rungumi manufofi da ’yan kasar suka amince, su kuma yi aiki kafada da kafada, wajen tabbatar da manufofin da za su amfani kasar.  (Saminu)