logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi tsokaci game da keta hakkin yara a Amurka

2022-03-16 10:42:30 CMG

Wakilin kasar Sin ya halarci taron tattaunawa game da kare hakkin yara, wanda zama na 49 na hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ya shirya a jiya Talata. Yayin zaman, wakilin ya zanta da wakilin musamman na babban sakataren MDD, game da irin muzgunawar da yara ke fuskanta a Amurka.

Wakilin na Sin ya ce mahukuntan Amurka, sun tsare yara kanana ’ya’yan ’yan ci rani tsawon lokaci a wasu cibiyoyin killacewa, wanda hakan ya haifar da cin zarafin yaran, da raba su da iyayen su da karfin tuwo.

Ya ce yaduwar kananan bindigogi a Amurka, ya haifar da yawan aukuwar harbe-harbe a makarantun kasar, inda yara masu yawan gaske suka sha fadawa hadari sakamakon hakan.

Wasu alkaluma sun nuna yadda a Amurka, adadin tashe-tashen hankula masu nasaba da harbin bindiga suka karu, da sama da kaso 30 bisa dari, yayin barkewar annobar COVID-19, kuma shi ma adadin yaran da aka harba da bindiga ya karu a asibitocin kasar.

A shekarar 2021 da ta gabata kadai, adadin Amurkawa da aka hallaka ta hanyar harbin bindiga ya kai mutum 44,750, ciki har da matasa da yara kanana ’yan kasa da shekaru 17 su 1,533. A dai shekarar ta bara, adadin mutanen da suka ji raunuka sakamakon harbin bindiga ya kai mutum 40,359, ciki har da matasa da yara kanana ’yan kasa da shekaru 17 su 4,107.

Don haka wakilin na Sin ya ja hankalin Amurka, da ta dauki kwararan matakai na shawo kan yaduwar kananan bindigogi, tare da aiwatar da ingantaccen tsari na kare hakkokin yara, da ma sauran rukunonin al’ummar kasar.  (Saminu)