logo

HAUSA

Majalisar dokokin Iraqi za ta zabi sabon shugaban kasa a watan Maris

2022-03-16 10:24:09 CMG

Majalisar dokokin kasar Iraqi ta sanar da cewa, za ta gudanar da taro domin zabar sabon shugaban kasa a ranar 26 ga watan Maris.

Bisa ga dokar tsarin mulkin kasar, ’yan majalisar dokoki ne za su zabi sabon shugaban kasar Iraqi daga cikin ’yan takara, ta hanyar kada kuri’ar kashi biyu bisa uku na adadin kujerun majalisar dokokin kasar 329, kuma shugaban kasar zai shafe wa’adin shekaru biyu zuwa hudu ne a karagar mulki.

Da zarar an zabe shi, sabon shugaban kasar zai bukaci babbar majalisar kasar ta ayyana sunan firaminista da zai jagoranci kafa gwamnati cikin kwanaki 30. (Ahmad)