logo

HAUSA

Wang Yi ya tattauna da ministan harkokin wajen Iran ta wayar tarho

2022-03-16 14:21:12 CMG

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna da ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian, ta wayar tarho a ranar 15 ga watan Maris.

Abdollahian, ya taya kasar Sin murnar kammala manyan tarukan shekara-shekara na kasar, kana ya bayyana ci gaba na baya bayan nan da aka samu game da dawowa tattaunawa kan batun aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran. Bangaren Iran ya godewa bangaren kasar Sin bisa muhimmiyar rawar da take takawa game da tattaunawar, kana yana fatan bangaren kasar Sin zai ci gaba da nuna goyon baya kan batun.

Wang Yi ya bayyana cewa, a ko da yaushe, kasar Sin tana goyon bayan cimma yarjejeniyar dawowa kan tattaunawar a kan lokaci, kofarta a bude take, kuma za ta ci gaba da ba da goyon bayanta ga dukkan wani kokarin da zai taimaka wajen cimma burin da aka sanya gaba. Kasar Sin ta fahimci hakikanin damuwar dake shafar hakkokin Iran, kana za ta goyi bayan Iran wajen tabbatar da kiyaye hakkoki da moriyarta, sannan tana adawa da dukkan matakan sanya takunkumi na bangare guda wanda ba shi da tushe a dokokin kasa da kasa. Bisa lura da tasirin wannan batu game da yanayin ci gaban kasa da kasa da na shiyya, kasar Sin a shirye take ta kara zurfafa hadin gwiwa da kuma yin aiki tare da Iran domin ingiza hanyoyin warware batutuwan dake shafar nukiliyar Iran a bisa hanya mafi dacewa don tabbatar da zaman lafiya da tsaron shiyyar. (Ahmad)