logo

HAUSA

Jakadan Sin a Najeriya ya gana da babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen kasar

2022-03-16 10:58:51 CMG

A ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2022, jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya gana da ambasada Dagali, babban daraktan kwamitin hadin gwiwar Afrika na ma’aikatar harkokin wajen Najeriya.

Ambasada Cui ya bayyana cewa, Sin da Najeriya suna da alakar siyasa ta kut-da-kut da muhimmiyar hadin gwiwa. A halin da ake ciki, hadin gwiwar Sin da kwamitin raya hadin gwiwar Sin da Najeriya yana kara samun bunkasuwa. Kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Najeriya domin zurfafa hadin gwiwar siyasa da amincewa da juna, da nufin gina ingantacciyar hadin gwiwa karkashin shawarar “Ziri daya da hanya daya,” don daga matsayin hadin gwiwar bangarorin biyu a fannonin samar da kayayyakin more rayuwa, da fannin sadarwa, da fasahohin aikin gona, da magungunan gargajiya, da sauransu, da kuma kara sabon kaimi ga ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Najeriya.

Dagali a nasa bangaren ya ce, kasar Sin babbar aminiya ce, kuma abokiyar hadin gwiwar Najeriya, sannan ta samar da taimako mai yawa ga tattalin arziki da ci gaban zaman rayuwar al’ummar kasar na dogon lokaci. A nan gaba kuma, ana fatan kara zurfafa hadin gwiwar tuntubar juna, da yin aiki tare da kasar Sin, domin aiwatar da yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka cimma matsaya kansu, da kuma sakamakon da aka samu a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, da kuma sa kaimi wajen tattauna karin ayyukan shiyyar wadanda ke da matukar alfanu ga ci gaban Afrika domin biyan muradun al’ummar nahiyar, don amfanawa ci gaban nahiyar da kyautata zaman rayuwar al’umma. (Ahmad)