logo

HAUSA

Rasha ta ayyana shirin ficewa daga majalissar Turai

2022-03-16 10:09:28 CMG

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha, ta sanar da shirin kasar na ficewa daga majalissar tarayyar Turai. Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a jiya Talata, ta ce Rasha ta mikawa ofishin babbar sakatariyar majalissar Marija Pejcinovic Buric, sako mai kunshe da wannan aniya.

Sanarwar ta kara da cewa, kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO, da kungiyar tarayyar Turai ta EU, suna cin zarafin mafi yawan kasashe mambobin hadakar, inda suka mayar da majalissar ta Turai wani makami na yiwa manufofin Rasha kafar ungulu. Kaza lika ba bu daidaito wajen gudanar da tattaunawa, yayin da ake ci gaba da watsi da asalin manufofin kafa hadakar.

Sai dai duk da hakan, Rasha ta ce za ta ci gaba da shiga tattaunawa bisa adalci, kan duk wasu batutuwa da suka shafi moriyar bai daya tsakaninta da majalissar ta Turai.

Tun a ranar Alhamis ne Rasha ta bayyana dakatar da shiga harkokin majalissar Turai, bayan da ta kasance mambar majalissar ta 39, a watan Fabarairun shekarar 1996.  (Saminu Hassan)