logo

HAUSA

Gwamnatin Masar ta sha alwashin dakile matsalar hauhawar farashin kayan abinci

2022-03-15 11:19:08 CRI

Yayin da watan Azumin Ramadan ke karatowa, mahukuntan kasar Masar sun sha alwashin aiwatar da wasu matakai, na rage hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwanni. Gwamnatin Masar dai ta alakanta karuwar farashin da aka samu a baya bayan nan, musamman na kayan abinci, da barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma karatowar watan Azumi.

Da yake karin bayani game da hakan a makon da ya gabata, firaministan kasar Mostafa Madbouly, ya ce farashin kayan amfanin gona kamar Alkama da kaji sun yi matukar tashi, tun bayan barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

Madbouly ya ce, gwamnatin Masar ta tsara sayar da kayan abinci da ‘yan kasar suka fi bukata, a farashi mai rahusa cikin watanni 6 masu zuwa, domin tausasawa jama’a. Ya ce gwamnati za ta fadada cibiyoyin sayar da kayan abinci mai rahusa a wurare dake kusa da jama’a. kaza lika za ta matsa kaimi wajen kula da farashi a kasuwanni, da yayata manufar tsumin abinci.

A ranar Lahadi, shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na Masar, ya ba da umarnin baiwa manoman kasar karin tallafin gata, domin karfafa musu gwiwar samar da karin Alkama, yayin noman damunar dake tafe, tun daga watan Afirilu mai zuwa.  (Saminu)