logo

HAUSA

Wakilan kasashen Ukraine da Rasha sun tsagaita tattaunawa

2022-03-15 10:31:41 CRI

Wakilan kasashen Ukraine da Rasha, dake tattaunawa domin shawo kan ricikin da ya barke tsakanin kasashen 2, sun dan tsagaita ganawa zuwa Talatar nan, bayan shafe tsawon sa’oi suna gudanar da shawarwari ta kafar bidiyo a jiya Litinin.

Da yake karin haske game da hakan, mashawarci ga shugaban kasar Ukraine, kuma memba a tawagar wakilan kasar Mykhailo Podolyak, ya ce an dau matakin dakatawar ne domin gudanar da wasu ayyuka, karkashin kananan rukunonin sassan biyu, da kuma tantance sharuddan da kowa ya gabatar.

Kafin hakan, Mr. Podolyak ya ce an gudanar da tattaunawa mai tsauri tsakanin tsagin Ukraine da Rasha, wadda ta zamo zagaye na 4 kafin a kai ga dakatawa.   (Saminu)