logo

HAUSA

Babban jami’in MDD ya sanar da sakin kudaden ayyukan jinkai a Ukraine

2022-03-15 10:37:13 CRI

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya sanar a jiya Litinin cewa, an fitar da kudi dala miliyan 40 daga babban asusun ayyukan gaggawa na hukumar ta kasa da kasa, domin samar da tallafi a kasar Ukraine.

A cewar babban sakataren, kudaden zasu taimaka wajen samar da muhimman kayayyakin jinkai da suka hada da abinci, da ruwa, da magunguna, da sauran kayan bukatun yau da kullum wadanda za a aika kasar Ukraine, kana za a samar da tallafin kudi ga mabukata.

Guterres, ya jaddada muhimmancin kiyaye dokokin ayyukan jinkai na kasa da kasa, inda ya bayyana cewa, a kalla mutane miliyan 1.9 ne suka tsere daga gidajensu a Ukraine, kuma adadin mutanen dake tserewa zuwa makwabtan kasashe yana ci gaba da karuwa.

Yace, MDD, da abokan hulda dake samar da tallafin jinkai, suna aiki tare domin tabbatar da ficewar fararen hula daga yankunan da sojoji suka mamaye tare da samar musu kayan tallafi a wuraren dake da tsaro. Sama da mutane 600,000 ne suka samu nau’ikan tallafin ya zuwa yanzu.(Ahmad)