logo

HAUSA

Xi ya taya Serdar Berdimuhamedov murnar zabensa a matsayin shugaban Turkmenistan

2022-03-15 20:24:40 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a Talatar nan ya aike da sakon taya murna ga Serdar Berdimuhamedov, bisa zaben da aka yi masa a matsayin shugaban kasar Turkmenistan.

A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a matsayinsa na makwabci mai sada zumunta, kuma abokin huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare na kasar Turkmenistan, bangaren kasar Sin yana matukar farin ciki da saurin ci gaban da Turkmenistan ta samu a fannin ginawa, da farfado da kasar, tun bayan da ta samu 'yancin kai shekaru 30 da suka gabata.