logo

HAUSA

Tawagogin Ukraine da Rasha sun dawo tattaunawar zaman lafiya

2022-03-15 21:10:09 CRI

Kafar yada labaran kasar Ukraine mai suna Ukrayinska Pravda ta ruwaito David Arakhamia, mamba a tawagar kasar ta Ukraine yana cewa, tawagogin Ukraine da Rasha sun koma teburin shawarwarin zaman lafiya a yau Talata.

Arakhamia ta sanar da cewa, an riga an fara tattaunawar sai dai ba ta yi wani karin bayani ba. Tawagogin kasashen biyu wato, Ukraine da Rasha sun fara zagaye na hudu na tattaunawar ce ta kafar bidiyo a ranar Litinin.

Mai ba shugaban kasar Ukraine shawara Mykhailo Podolyak, kana memba a tawagar tattaunawar, ya ce bangarorin biyu, sun dan dakatar da tattaunawar har zuwa yau Talata, domin gudanar da wasu ayyuka, karkashin kananan rukunonin sassan biyu, da kuma tantance sharuddan da kowa ya gabatar.