logo

HAUSA

An ayyana ranar gudanar da babban zaben kasar Saliyo

2022-03-15 10:33:05 CRI

A jiya Litinin ne hukumar zaben kasar Saliyo, ta ayyana ranar 24 ga watan Yunin shekarar 2023, a matsayin ranar da za a kada kuri’a, a zaben shugaban kasar dake tafe.

Kwamishinan hukumar zaben Mohamed Konneh ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai, wanda ya gudana a birnin Freetown, fadar mulkin kasar, inda ya ce baya ga zaben shugaban kasa, za kuma a gudanar da zabukan ‘yan majalissar dokokin kasar da kansiloli.

Konneh ya ce tuni hukumar zaben ta tsara fara yin rajistar masu zabe, tun daga ranar 3 ga watan Satumbar zuwa 4 ga watan Oktobar wannan shekara.  (Saminu)