logo

HAUSA

Mene ne sirrin dake tattare da dakuna 336 na gwajin halittu da Amurka ta mallaka a fadin duniya

2022-03-14 14:07:48 CRI

Rahotanni na cewa rikicin da ake tsakanin Rasha da Ukraine, ya bankado wasu batutuwa da ba a yi tsammani ba. Kafafen yada labarai na kasar Rasha sun ruwaito cewa, ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon, ta kaddamar da sama da dakunan 30 na gwajin kwayoyin halittu a Ukraine, inda aka adana wani adadi mai yawa na kwayoyin cuta masu hadari.

Shi ya sa ake ganin Amurka ta nace sai an nemo asalin kwayar cutar COVID-19 a dakunan gwaji na kasar Sin. Wataklila saboda kasancewar ta na da dakunan gwaji a fadin duniya, tana sane da irin hadarin dake tattare da zurerwar kwayoyin cuta da barkewar annoba.

Rahotanni a baya bayan nan, sun bayyana cewa, ofishin jakadancin Amurka a Ukraine ya yi gaggawar goge wasu bayanai game da dakunan gwajin kwayoyin halittu dake kasar. Sai dai ba za su iya goge shaidu game da kasancewar irin wadannan dakuna a fadin duniya ba. Lokaci ya yi da ya kamata Amurka ta wallafa bayanai game da wadannan dakunan gwaji, da nau’ikan kwayoyin halittu da aka adana a cikinsu da irin nau’in binciken da ake gudanarwa da illolinsu ga jama’ar kasashen da dakunan gwajin suke a fadin duniya. Duniya na bukatar amsa. (Fa’iza)