logo

HAUSA

Mutane akalla 75 sun mutu sanadiyyar hatsarin jirgin kasa a DRC

2022-03-14 10:22:29 CRI

Mutane akalla 75 sun mutu, yayin da wasu 125 suka jikkata sanadiyyar gocewar jirgin kasa daga kan layin dogo a yankin kudu maso gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC.

Darakta janar na kamfanin kula da sufurin jiragen kasa na kasar, Fabien Mutomb, ya ce gocewar jirgin mai tarago 15, ta auku ne da yammacin ranar Alhamis a gundumar Lubudi na lardin Lualaba dake kudu maso gabashin kasar.

A cewar ma’aikatar yada labarai ta kasar, jirgin ya rasa iko da taragonsa da dama, inda ya fada cikin wani kwazazzabo saboda lalacewar inji.

Ana samun rahoton hadduran jiragen kasa a wannan yanki na kasar saboda rashin kyan yanayin jiragen da kuma layukan dogo. (Fa’iza Mustapha)