logo

HAUSA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Sin ta tambayi Amurka kan dakin gwaje-gwajen halittunta dake Ukraine

2022-03-14 21:09:17 CRI

Dangane da batun dakin gwaje-gwajen kwayoyin halittu na Amurka da ke Ukraine, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Litinin cewa, bayan da Rasha ta gano wasu takardu, da hotuna, gami da shaidu na zahiri a Ukraine, bangaren Amurka ya yi amfani da kalmar "bayanan karya" don gyara abubuwan da suka gabata, wanda zai yi wahala ta gamsar da jama'a.

Rahotanni sun nuna cewa, a ranar 11 ga wata ne, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya gudanar da wani taro don duba batun tsaron kwayoyin halittun dake wadannan dakuna a Ukraine. Wakiliyar din din din ta kasar Amurka a MDD Linda Thoms-Greenfield ta bayyana cewa, wai kasar Sin na yada labaran karya don tallafawa kasar Rasha.

Yayin da yake amsa tambayoyin da suka shafi wannan batu, Zhao Lijian ya ce, Amurka a ko yaushe tana tallar abin da ake kira “'gaskiya a bayyane”. Idan Amurka ta ce, wannan “bayanan karya ne”, to me ya sa ba ta ba da cikakkun bayanai don tabbatar da cewa ba ta da laifi? Ina dala miliyan 200 din da Amurka ta kashe? Wane bincike Amurka ta gudanar a kan wadanne cututtuka? Ofishin jakadancin Amurka a Ukraine ya goge duk wasu bayanan da suka shafi wannan batu a shafinsa na intanet, me suke kokarin boyewa? Me ya sa Amurka ke adawa da kafa tsarin bincike na bangarori da dama na Yarjejeniyar Makamai masu guba a cikin tsawon shekaru 20 da suka gabata? Idan Amurka tana son wanke kanta, me ya sa ba ta bude wadannan dakunan gwaje-gwaje na kwayoyin halittu ga kwararru na kasa da kasa don su gudanar da bincike ba? (Mai fassara: Bilkisu Xin)