logo

HAUSA

Sashen hidimar sufuri na Sin ya samu ci gaba a watanni 2 na farkon bana

2022-03-14 13:45:31 CRI

Cibiyar kimiyya ta ma’aikatar sufurin kasar Sin, ta fitar da alkaluman hidimar sufurin kasar na watannin Janairu da Fabarairun bana, alkaluman da suka nuna bunkasar fanni da maki 153.8, karuwar da ta kai ta kaso 4.4 bisa dari, sama da makamancin lokaci a bara.

A cewar cibiyar alkaluman na CTSI, bangaren dakon hajoji, sun bunkasa sosai a watannin 2 na farkon shekara, inda matsakaicin makin su ya kai 188.2, wanda ya nuna karuwar kaso 4.1 bisa dari, wanda hakan ya nuna farfadowar fannin da kaso 2.2 bisa dari daga watan Disambar bara, karin da shi ne mafi yawa da aka samu cikin watanni 6.

Har ila yau, matsakaicin alkaluman CTSI na dakon fasinjoji, ya kai maki 83.8 a tsakanin watannin biyu, karuwar da ta kai ta kaso 4.7 bisa dari.

Alkaluman hidimar sufurin kasar Sin ko CTSI, yana auna adadin hidimar da sufurin fasinja, da na dakon kayayyaki ke samarwa, ta bangaren layukan dogo, da manyan hanyoyin mota, da na ruwa, da fannin jiragen sama. Yana kuma kunshe da cikakkun bayanai game da fannin sufurin kasar baki daya.   (Saminu)