logo

HAUSA

Tsohon shugaban Amurka ya harbu da cutar COVID-19

2022-03-14 10:05:32 CRI

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya harbu da cutar COVID-19. Obama ya bayyana a jiya Lahadi cewa, gwajin da aka yi masa ya tabbatar da harbuwarsa. Amma ya ce shi da mai dakinsa Michelle Obama, sun yin farin ciki da kasancewa tuni sun karbi rigakafin cutar, kuma gwajin da aka yiwa mai dakin sa ya nuna ba ta dauke da cutar.

Obama ya ce “Wannan tamkar matashiya ce game da bukatar kowa ya karbi rigakafi idan har bai riga ya karba ba, duk kuwa da raguwar da aka samu ta masu harbuwa da annobar.”

Obama wanda a yanzu ke da shekaru 60, ya kasance shugaban Amurka na 44, tsakanin shekarun 2009 zuwa 2017.

Alkaluman jami’ar Johns Hopkins suka bayyana cewa, ya zuwa yammacin jiya Lahadi, adadin mutanen da suka harbu da annobar COVID-19 a Amurka, ya kai sama da mutane miliyan 79, inda tuni cutar ta hallaka mutane 967,000.  (Saminu)