logo

HAUSA

Jakadan Sin zai gana da mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka

2022-03-14 10:13:42 CRI

Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS Yang Jiechi, zai gana da Jake Sullivan, mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka a birnin Roma na Italiya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya sanar da cewa, Yang Jiechi, wanda kuma shi ne daraktan ofishin hukumar kula da harkokin waje, ta kwamitin tsakiyar, zai yi musayar ra’ayi da Jake Sullivan, kan dangantakar kasashensu da batutuwan yankunan da ma wadanda suka shafi duniya baki daya.

A cewar kakakin, jigon ganawar shi ne, aiwatar da muhimman yarjeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin ganawarsu ta kafar bidiyo a watan Nuwamban bara.

Ya kara da cewa, tun daga wancan lokaci ne bangarorin biyu ke tuntubar juna game da taron tare da sanya lokacin da ya dace na gudanar da shi. (Fa’iza Mustapha)