logo

HAUSA

Fitch: Kamfanonin jigilar da kayayyaki cikin sauri na Sin za su kafa dunkulewa nan da shekaru masu zuwa

2022-03-14 14:38:12 CRI

Cibiyar lura da hada hadar kudade ta Fitch, ta ce cikin shekaru masu zuwa, kamfanonin jigilar da kayayyaki cikin sauri na kasar Sin za su ci gaba da dunkulewa, ta hanyar hadaka da kuma mallakar karin kadarori da kamfanoni kanana masu inganci.

Cibiyar ta ce tun daga shekarar 2021, irin wadannan kamfanoni na kasar Sin sun hade da wasu, ciki har da kamfanonin JD da SF, wadanda suka mallaki wasu kamfanonin domin fadada harkokin kasuwancin su.

Fitch ta yi hasashen karuwar takara mai tsanani cikin matsakaicin lokaci, yayin da manyan kamfanonin dake fannin ke fadada ikon su cikin hanzari, domin samun moriyar bunkasa tattalin arziki, da fadadar hannayen jarin su a kasuwanni.

A cewar kamfanin gidan waya na kasar Sin, adadin kudin shiga a fannin jigilar da kayayyaki cikin sauri zai karu da kaso 11 bisa dari a bana, inda darajar kudaden sa za ta kai kudin Sin tiriliyan 1.4, kimamin dalar Amurka biliyan 219.6 ke nan a shekara.  (Saminu)