logo

HAUSA

Majalisar gudanarwar Sin ta aike da sakon taya murna ga tawagar 'yan wasan kasar da suka halarci gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing

2022-03-13 18:02:55 CRI

A yau Lahadi, majalisar gudanarwar kasar Sin ta aike da sakon taya murna ga tawagar 'yan wasan kasar da ta halarci gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi karo na 13 ta Beijing.

Sakon taya murnar ya ce, “A wajen gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi karo na 13 da aka yi a Beijing, tawagar kasar Sin ta yi gwagwarmaya sosai tare da samun lambobin zinare 18, da na azurfa 20, da na tagulla 23, inda ta zama ta farko a jerin sunayen lambobin zinare da na lambobin yabo, hakan ya nuna ta samu sakamako mafi kyau a tarihin kasar na halartar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi, da samun karramawa ga kasar da al'ummarta, da ba da gudummawa sosai wajen samun nasarar karbar bakuncin gasar. Kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS da majalisar gudanarwar kasar suna mika sakon taya murna da gaisuwa a gare ku!”

Sakon ya kuma nuna cewa, bajintar da ‘yan tawagar suka yi na nuna cikakken ruhin wasannin motsa jiki na kasar Sin, kuma yana nuna cikakken nasarorin da kasar ta samu wajen kare hakkin dan Adam da ci gaban kasa, kana da kara zaburar da kishin kasa na ’ya’yan kasar Sin maza da mata dake gida da waje, da sanya karfin ruhi ga daukacin jam'iyyar JKS da jama'ar kabilu daban daban ta kasar wajen hada kai don kara raya kasa mai tsarin gurguzu na zamani. (Mai fassara: Bilkisu Xin)