logo

HAUSA

Mataimakiyar firaministan Sin ta bukaci a dauki matakan dakile cutar COVID-19 cikin kankanin lokaci

2022-03-13 16:08:28 CRI

Mataimakiyar firaministan kasar Sin, Sun Chunlan, ta bukaci yankunan dake fama da tsananin yaduwar annobar COVID-19 su yi kokarin dakile cutar a cikin kankanin lokaci.

Sun, ta yi wannan tsokaci ne a wajen taron majalisar gudanarwar kasar ta wayar tarho game da matakan yaki da annobar COVID-19.

Ta bukaci a dauki kwararan matakan dakile annobar cikin hanzari.

Sun ta ce, ya kamata a kara kokarin fadada ayyukan gwaje-gwajen cutar, da fadada ayyukan tantance yanayin lafiyar jama’a, da aikin jigilar marasa lafiyar da kuma aikin killacewa.

Ta kara da cewa, ya kamata a bayar da fifiko wajen kandagarkin hana shigo da cutar daga ketare, inda bangaren tashoshin ruwa zasu kasance a matsayin ginshiki.

Sun ta kuma bukaci makarantu da su karfafa ayyukan binciken lafiya dake gudana a kullum, a kara yawan adadin gwajin cutar da ake gudanarwa, da kuma samar da matakan kariya daga fuskantar yaduwar cutar.(Ahmad)