logo

HAUSA

Tsarin BeiDou na kasar Sin ya shiga sabon yanayi na ayyukan hidimomi da da saurin cigaba

2022-03-13 17:16:30 CRI

Tsarin amfani da tauraron dan adam dake samar da hidimomin taswirar yankunan ta BeiDou na kasar Sin wato (BDS), ya shiga sabon matakin samar da ayyukan hidimomi mai dorewa, da kuma samun bunkasuwa cikin sauri, kamar yadda ofishin kula da tauraron dan adam mai nuna taswirar yankuna na kasar Sin ya bayyana.

Ofishin ya ce, bisa lura da tsarin bibiya na duniya, tsarin BDS-3 ya samu gagarumin cigaba wajen samar da hidimomin taswira da bibiyar wurare a duniya, yayin da kuma ake da adadi mai matukar yawa da ake son gudanarwa a yankin Asiya da Pacific.

Sanarwar ofishin ta kara da cewa, kamar yadda aka tsara, za a kaddamar aikin sabbin tauraron dan adam na BDS, don kara fadada tsarin domin samun inganci da kuma tabbaci, kana za a gudanar da sabbin gwaje-gwajen fasaha da kuma tantancewa, domin tabbatar da cigaba da daga matsayin tsarin amfani da wannan fasaha.

A ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2020, kasar ta kaddamar da tsarin BDS a hukumance, kuma ta bude sabon tsarin BDS-3 ga masu amfani da tsarin a duniya.

A cewar ofishin, tun daga wancan lokacin, tsarin BDS ya cigaba da sa kaimi wajen samar da ingantattun hidimomi don biyan bukatun masu amfani da tsarin a duniya. Bugu da kari, tsarin ya ci gaba da inganta ayyukansa tare da fadada tsarin amfani da manhajojinsa yadda ya kamata. (Ahmad)