logo

HAUSA

An samu sabbin masu kamuwa da COVID-19 1,938 a babban yankin Sin

2022-03-13 17:33:13 CRI

Babban yankin kasar Sin ya tabbatar da sabbin alkaluman masu kamuwa da cutar COVID-19 kimanin 1,938 a ranar Asabar, daga cikinsu akwai mutane 1,807 da suka kamu da cutar a cikin gida, ragowar mutane 131 kuma suka shigo da cutar daga kasashen ketare, kamar yadda alkaluman da hukumar lafiyar kasar ta bayyana a yau Lahadi.

Kimanin sabbin mutane 1,455 aka samu sun kamu da cutar ba tare da nuna alamomin cutar ba, yayin da majinyata 6,287 ne ke karkashin kulawar likitoci wadanda basu nuna alamomin kamuwa da cutar ba.

A halin yanzu, jimillar mutanen da suka kamu da cutar a babban yankin kasar Sin ya kai 115,466, inda adadin mutanen da suka mutu bai canza ba wanda ya kai 4,636, tun a watan Janairun shekarar bara.(Ahmad)