logo

HAUSA

Shugaban IPC ya ayyana rufe gasar Olympic ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta Beijing

2022-03-13 21:50:35 CRI

Shugaban kwamitin shirya gasar Olympic ajin nakasassu ta lokacin sanyi na kasa da kasa (IPC), Andrew Parsons, ya bayyana rufe gasar Olympic ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 a yammacin yau Lahadi.

A yayin da yake gabatar da jawabi a bikin rufe gasar, a babban filin wasa na kasar Sin, Parsons ya bayyana cewa, gasar Beijing 2022 ta kafa wani sabon tarihi a gasar Olympic ajin kasassu ta lokacin sanyi.

Shugaban na IPC ya ce, “Abin burgewa ne yadda aka shirya gasar, filayen wasa masu kayatarwa, da wasanni masu cike da tarihi, duk wadannan an samu a lokacin muhimmiyar gasar ta Beijing. Tabbas ne, kasar Sin ta samar da abin koyi ga daukacin tsarin gasar wasannin Olympic ajin nakasassu ta lokacin hunturu wadanda zasu gudana a nan gaba. Hakika, a yanzu kasar Sin ta zama jigon wasannin Olympic ajin nakassu ta lokacin sanyi.”

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya halarci bikin rufe gasar.

A yayin bikin rufe gasar, an kuma mika tutar gasar Olympic ajin kasassu ta lokacin sanyi ga jami’an biranen Milan da Cortina d'Ampezzo, wadanda za su karbi bakuncin gasar Olympic ajin kasassu ta lokacin sanyi a shekarar 2026.

Beijing, ya kasance birni na farko a duniya da ya kafa tarihin karbar bakuncin gasar wasannin Olympic ajin nakasassu ta lokacin zafi da ta sanyi.(Ahmad)