logo

HAUSA

Mataimakin ministan harkokin wajen Sin ya tattauna da takwaransa na Najeriya

2022-03-12 15:37:23 CRI

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Deng Li, ya ce cikin shekaru sama da 50 da suka gabata, wato tun bayan daddale huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, fahimtar juna a bangaren siyasa tsakanin sassan biyu na kara zurfafuwa a kai a kai, haka kuma huldar dake tsakaninsu, ta samu ci gaba yadda ya kamata.

Deng Li ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin siyasa da harkokin waje na gwamnatocin Sin da Najeriya da ya gudana ta kafar bidiyo tare da karamin ministan harkokin wajen Najeriya, Zuberu Dada.

A cewarsa, kwamitin na gwamnatocin kasashen Sin da Najeriya, tsari ne na farko da aka kafa tsakanin gwamnatin kasar Sin da gwamnatin kasashen Afirka, lamarin da ya nuna cewa, sassan biyu wato Sin da Najeriya, suna mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninsu. Ya ce kasar Sin tana cike da imani kan makomar ci gaban dangantakar sassan biyu, kuma tana son hada hannu da Najeriya, domin ciyar da huldarsu gaba.

A nasa bangaren, Zuberu Dada ya bayyana cewa, kasarsa tana ba da muhimmanci sosai ga huldarta da kasar Sin, kuma tana nacewa kan manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, kana tana son kara karfafa goyon bayansu ga juna, cikin harkokin kasa da kasa. Ban da haka kuma, tana son kara karfafa hadin gwiwarta da kasar Sin a fannoni daban daban. (Jamila)