logo

HAUSA

Kasar Sin: dole ne a warware matsalolin dukkan bangarori yayin da ake tattauna batun nukiliyar Iran

2022-03-12 16:05:41 CRI

 

Zaunannen wakilin Sin a ofishin MDD dake Vienna, Wang Qun ya ce wajibi ne a duba bukatun dukkan bangarori tare da shawo kansu, yayin da ake tattauna batun nukiliyar Iran.

Wang Qun ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake gabatar da jawabi a dakin taron tattauna batun nukiliyar Iran, a Vienna na kasar Austria.

Jakadan ya bayyana haka ne, bayan Tarayyar Turai ta sanar da tsahirta tattaunawar ta Vienna, da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, saboda wasu batutuwa.

Karkashin yarjejeniyar ta 2015, Iran ta amince da wasu daga cikin haramcin da aka yi mata na raya shirin nukiliyarta, domin MDD da kasashen yamma su dage takunkuman da suka kakaba mata.

Sai dai, tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya janye kasarsa daga yarjejeniyar a shekarar 2018, inda ya sake kakabawa Iran din karin takunkumai. Ita kuma Iran ta mayar da martani ta hanyar soke wasu daga cikin alkawurran da ta yi. (Fa’iza Mustapha)