logo

HAUSA

Faduwar darajar kudin Sudan ta durkusar da manyan kasuwanni a Khartoum

2022-03-12 17:00:05 CRI

 

Kasuwanni a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, na fuskantar wani yanayi na rudani saboda faduwar darajar kudin kasar a kasuwar musayar kudaden waje.

Wani rangadi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi a kasuwar Al-Sajana dake yammacin birnin Khartoum, da kasuwar khartoum 2 dake tsakiyar birnin, da kuma babbar kasuwar birnin dake yankin kudanci, ya bayyana cewa, galibin shaguna sun daina sayar da kayayyaki saboda gazawa wajen tantance farashinsu.

A ranar Talatar da ta gabata ne, babban bankin kasar ya ba bankuna da kamfanonin musayar kudi damar tsayar da farashinsu na musayar kudaden ketare ba tare da sa bakin babban bankin ba.

Sudan ta shiga matsalar tattalin arziki ne bayan Amurka da hukumomin kasashen wajen sun dakatar da bayar da taimako da dala miliyan 100, bayan Abdel Fattah Al-Burhan, shugaban rundunar sojin kasar, ya ayyana dokar ta baci tare da rushe gwamnatin rikon kasar a ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata. (Fa’iza Mustapha)