logo

HAUSA

AU: babban dakin adana kayayyakin tarihi zai yayata tare da kare al'adun gargajiya na nahiyar Afrika

2022-03-12 16:00:16 CRI

 

Tarayyar Afrika AU, ta ce burin babban dakin adana kayayyakin tarihi na Afrika shi ne karewa da yayatawa tare da raya al'adun gargajiya na nahiyar.

Kwamishinar kula da lafiya da harkokin jin kai da walwalar jama'a ta AU, Cessouma Minata Samate ce ta bayyana haka, yayin kaddamar da dakin wucin gadi na adana kayayyakin tarihi na nahiyar.

Ta kuma nanata bukatar yayata fasahohi da al'adun gargajiya na nahiyar, tana mai cewa, babban dakin na wucin gadi da zai gudanar da shirye-shirye masu ruwa da tsaki, zai taka muhimmiyar rawa a wannan bangare, inda ta ce sun kaddamar da mazauni na wucin gadi na dakin ne kafin kammala gini na dindin din tare da kaddamar da shi.

Ana shirya kaddamar da dakin adana kayayyakin tarihin ne a shekarar 2023 a matsayin wani bangare na aiwatar da kashin farko na wa'adin shekaru 10, na ajandar raya nahiyar na shekaru 50 da ake son cimmawa zuwa shekarar 2063.

Dakin adana kayayyakin tarihin da zai samu mazauni a Algiers babban birnin Algeria, zai nuna tare da karewa da kuma yayata dimbin al'adun gargajiya na nahiyar. (Fa’iza Mustapha)