logo

HAUSA

Li Keqiang: Inganta manufar samar da guraben aikin yi a kasar Sin

2022-03-11 13:49:01 CRI

 Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau Juma’a a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kyautata manufar samar da guraben aikin yi sannu a hankali, da inganta hakkin ‘yan kwadago a bangarori daban-daban da ba da tabbaci ga rayuwar al’umma da sauransu.

Li Keqiang ya ce, a halin da ake ciki, yawan ‘yan kwadago masu zaman kansu a ayyuka daban-daban, ya kai miliyan 200. A matsayinta na kasa mai tasowa, za a samu irin wadannan ‘yan kwadago masu zaman kansu a kasar Sin cikin dogon lokaci. A bana kuma, gwamnatin tana kara kaimi wajen aiwatar da manyan tsare-tsare, da aiwatar da manufofin kudi ta hanyar tabbatar da samar da guraben aikin yi, kana ya kamata a kara kaimi kan sauran manufofi, don cimma burin da aka tsaya game da samar da aikin yi. (Amina Xu)