logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ke bude kofa ga kasashen waje wata dama ce da ba za ta taba rufewa ba

2022-03-11 13:58:22 CRI

 

Fraministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, yanayin kasa da kasa ya kasance mai sarkakkiya da dagulewar al’amura tun lokacin da ya kama aiki, yayin da ake fuskantar sabani da matsaloli a cikin gida. Babban kalubalen shi ne, annobar COVID-19 da yadda ta yi mummunan tasirin ga tattalin arzikin kasar. Duk da haka, mun yi iya kokarinmu.

Li Keqiang ya bayyana cewa, kamata ya yi gwamnatin kasar Sin ta mayar da hankali wajen tabbatar da kyautata rayuwar jama'a da nufin bunkasa tattalin arziki, da kara mayar da hankali wajen neman gaskiya da shaidu na zahiri da sauraron muryoyi da bukatun jama’a

Firaminista Li ya ce, kasar Sin ta samu ci gaban kanta, da amfanar da jama’a da ma duniya baki daya, tun lokacin da ta bude kofarta ga kasashen waje fiye da shekaru 40. Wannan wata muhimmiyar dama ce da kasar ba za ta taba rufewa ba, kuma tilas ba za ta rufe ba. (Ibrahim)