logo

HAUSA

Kafofin intanet na kasar Sin na fuskantar hare-hare daga ketare

2022-03-11 16:30:41 CRI

Binciken da cibiyar dake lura da ayyukan daukin gaggawa a kafofin intanet na kasar Sin ta gudanar ya gano cewa, tun daga karshen watan Fabrairu, kafofin yanar gizo na kasar Sin suna ci gaba da fuskantar hare-haren masu kutse ta intanet daga kasashen ketare. Kungiyoyin dake sarrafa na’urorin kwamfuta suna iya sarrafa na’ura mai kwakwalwa a kasar Sin ta hanyar kai hare-hare, kuma sun kaddamar da irin wadannan hare-haren intanet kan kasashen Rasha, da Ukraine, da Belarus. Bayan gudanar da bincike, an gano cewa, an kaddamar da galibin wadannan hare-haren ne daga kasar Amurka, kuma an samu hare-haren sama da guda 10 daga jihar New York kadai.

An ba da rahoton cewa, cibiyar dake lura da ayyukan daukin gaggawa ta shafin intanet na kasar Sin ta riga ta magance wadannan hare haren ta intanet ba tare da bata lokaci ba.(Ahmad)