logo

HAUSA

Xi ya taya Yoon Seok-youl bisa zabensa a matsayin shugaban Koriya ta Kudu

2022-03-11 18:57:06 CRI

A ranar 10 ga watan nan na Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Yoon Seok-youl, bisa zabensa a matsayin shubagan kasar Koriya ta Kudu, inda ya X nuna cewa, Sin da Koriya ta Kudu makwabta ne, kuma muhimman abokan hadin gwiwa ne na juna. Tun bayan kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninsu, huldarsu ta bunkasa cikin sauri, wanda hakan ya haifar da alheri na zahiri ga al’ummun kasashen biyu, tare da bayar da gundumawa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma bunkasuwa da wadatar duniya. Bana ake cika shekaru 30 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Koriya ta Kudu, wanda hakan ke da muhimmiyar ma’ana ga huldar dake tsakanin sassan biyu.

Kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwar sada zumunta tsakaninta da Koriya ta Kudu, ta yadda za a ciyar da huldar sassan biyu gaba cikin lumana, tare da kawo alheri ga al’ummun kasashen biyu. (Safiya)