Li Keqiang: Saukaka biyan haraji hanya ce mafi inganta kasuwanci
2022-03-11 13:52:48 CRI
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana a yau Juma’a cewa, rage kudaden haraji ya kasance a matsayin hanya mafi dacewa da kuma inganci da za ta taimakawa ci gaban kasuwanci.
Li, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ba da fifiko ga kananan masana’antu a tsarin mayar da wani kaso na kudaden haraji domin taimaka musu wajen rage wahalhalu.(Ahmad)