logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun lalata haramtattu matatun mai guda 30

2022-03-11 11:16:55 CRI

 

            

Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar sojin kasar ta sanar da lalata wasu wuraren tace man fetur guda 30 ba bisa ka'ida ba a cikin makwanni biyun da suka gabata, a yankin Delta mai arzikin man fetur.

Mai magana da yawun rundunar sojojin kasar ta Najeriya Bernard Onyeuko, ya shaidawa manema labarai cewa, sojojin sun yi nasarar lalata bututun mai guda 57, tare da kame masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa 25 a lokacin samamen.

Onyeuko ya ce, an kuma kwato kayayyaki da dama a yayin gudanar da ayyukan, wadanda suka hada da jimillar lita miliyan 2.8 na danyen mai, da lita miliyan 3.8 na gas. (Ibrahim)