logo

HAUSA

Karamin Kwamitin Siyasa Da Diflomasiyya Na Babban Kwamitin Tsakanin Sin da Najeriya Ya Gudanar Da Taronsa Na Farko

2022-03-11 10:23:12 CRI

A ranar 10 ga watan Maris, karamin kwamitin siyasa da diflomasiyya na babban kwamitin tsakanin kasashen Sin da Najeriya ya gudanar da taronsa na farko ta kafar bidiyo, wanda Deng Li, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, da Zubairu Dada, karamin ministan harkokin wajen Najeriya suka jagoranta.

Bangarorin biyu sun yi nazari kan ci gaban da aka samu game da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan batun aiwatar da sakamakon da aka samu a taron ministoci karo na 8 na taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, kana sun zurfafa musayar ra’ayi game da batun karfafa huldar siyasa, da taimakawa juna tsakanin bangarori daban-daban, da kuma fadada hadin gwiwarsu a kananan ofisoshin jakadanci na kasashen biyu.

Bangarorin biyu za su aiwatar da ra’ayi daya da shugaba Xi Jinping, da shugaba Muhammadu Buhari suka cimma, game da bunkasa huldar kasashen biyu, da ingiza matakan aiwatar da sakamakon da aka samu a taron FOCAC, da ci gaba da zurfafa hakikanin hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, da kuma daga matsayin muhimmiyar huldar dake tsakaninsu zuwa matsayin koli.(Ahmad)