logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin yana fatan samun sauki kan halin da ake ciki a Ukraine

2022-03-11 11:41:06 CRI

 

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana fatan ganin halin da ake ciki a kasar Ukraine ya samu sauki, har ma zaman lafiya ya dawo cikin hanzari. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimakon jin kai ga Ukraine. Haka kuma kasar Sin tana goyon bayan duk wani kokarin da ake da zai kai ga warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar lumana.

Firaministan na Sin ya ce, takunkuman da aka kakaba, za su yi illa ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Don haka, ya kamata a yi kokarin ganin kasashen Rasha da Ukraine, su ci gaba da shawarwarin tsagaita bude wuta. Kasar Sin ta yi kira da a yi taka tsantsan, tare da hana ta’azzarar bala'in jin kai a Ukraine.(Ibrahim)