logo

HAUSA

Gasar Paralympics ta Beijing ta 2022 na nuni ga tasirin tunanin samun damammaki

2022-03-11 20:10:56 CRI

Kakakin kwamitin BOCOG mai shirya gasar Olympics ta birnin Beijing ajin nakasassu ko Paralympics Yan Jiarong, ta ce gasar dake gudana yanzu haka a birnin Beijing, na nuni ga tasirin tunanin samun damammaki.

Yan Jiarong ta yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana, yana mai cewa, irin wannan tunani muhimmin ginshiki ne na magance rashin samun damammaki, da kuma bunkasa shigar dukkanin sassa cikin harkokin wasanni.  (Saminu)