Muryar WHO ta sake fallasa asirin Amurka na mallakar dakin gwaje gwajen kwayoyin halittu masu guba a Ukraine
2022-03-11 19:51:40 CRI
Wasu rahotanni daga kafafen yammacin duniya, sun nuna yadda hukumar lafiya ta duniya WHO, a baya bayan nan, ta yi kira da mahukuntan kasar Ukraine, da su gaggauta lalata dakin gwajin kwayoyin halittu masu guba dake kasar, domin kaucewa bullar cutuka masu hadari, sakamakon yaki dake wakana a kasar.
Yayin da dakarun sojin Rasha suka bayyana cewa, sun gano bayanai masu alaka da shirin binciken kwayoyin halittu masu guba, da Amurka ke daukar nauyi a Ukraine, sassan kasa da kasa na tambayar dalilin da ya sanya Amurka aiwatar da wannan shiri.
A jiya Alhamis ne dai ma’aikatar tsaron kasar Rasha, ta fitar da wasu bayanai, dake nuna yadda Amurka da mambobin kungiyar tsaro ta NATO, ke daukar nauyin binciken makamai masu guba, a wata cibiyar gwaje gwaje dake Ukraine. (Saminu)