logo

HAUSA

Majalisar dokokin kasar Sin ta gudanar da taron rufe taron shekara-shekara

2022-03-11 09:37:50 CRI

 

Da safiyar yau ne, aka gudanar da taro na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da wasu jagororin kasar sun halarci taron da ya gudana a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin

A yayin taron rufe taron, 'yan majalisar dokokin, sun amince da wani kuduri kan rahoton aikin gwamnati, inda suka amince da yin kwaskwarima ga dokar majalisar wakilan jama’ar kananan hukumomi da ta gwamnatocin al’ummun kananan hukumomi.

Wakilan sun amince da shawarar da aka yanke, game da kaso da zaben wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14, sun kuma amince da hanyoyin da yankunan musamman na Hong Kong da Macao za su zabi wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14.

'Yan majalisar dokokin kasar Sin, sun kuma amince da babban kasafin kudin shekarar 2022 da shirin raya tattalin arzikin kasa da zamantakewa na shekarar 2022.

Haka kuma wakilan sun zartas da kuduri kan rahoton aiki na kotun kolin al’umma da rahoton aiki na kotun kolin gabatar da kararraki ta al’umma.(Ibrahim)