logo

HAUSA

Sin za ta dauki matakan kandagarkin COVID-19 bisa halin da kasar ke ciki

2022-03-11 13:48:24 CRI

 

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau Juma’a cewa, Sin tana aiwatar da matakan kandagarkin cutar COVID-19 da raya tattalin arziki da zaman al’ummar kasa tare, da kuma ingiza hadin kan kasa da kasa, Sin za ta dauki matakan kandagarkin bisa halin da ake ciki da yanayin kwayar cutar, ta yadda za a yi yaki da annobar bisa kimiyya da ba da tabbaci ga lafiyar jama’a da rayuwarsu da tsaron tsarin samar da kayayyaki. A halin yanzu kuma, akwai bukatar hadin kan kasa da kasa da yin hakuri da juna don samar da sharadi mai don ganin duniya ta koma daidai yadda ake fata. (Amina Xu)