logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci a rage gibin rigakafin COVID-19 yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD

2022-03-11 19:15:57 CRI

A jiya Alhamis, wakilin kasar Sin ya yi kira da a aiwatar da matakan cike gibin dake akwai a fannin rigakafin cutar COVID-19 tsakanin sassan duniya daban daban.

Wakilin na Sin ya yi kiran ne, yayin zama na 49 na hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, wanda aka shirya domin tattauna damar da kasashe ke da ita, ta samun isasshen rigakafi.

Wakilin na Sin ya ce, boye rigakafin da wasu kasashen yammacin duniya kalilan ke yi sama da bukatun su na gida, da kuma barnar sa da wasu ke yi ya kazanta, wanda hakan ke shafar adadin masu samun rigakafin a kasashe masu tasowa.

Kaza lika wakilin ya ce, ya zuwa yanzu, Sin ta samar da adadin rigakafin COVID-19 sama da biliyan 2.1, ga kasashe da hukumomin kasa da kasa sama da 120. Kuma Sin za ta samar da rigakafin har biliyan daya ga kasashen Afirka, ciki har da miliyan 600 kyauta ga nahiyar.  (Saminu)