logo

HAUSA

Kasar Sin ta mika dukkanin gudummawar rigakafi da ta samar wa ‘yan gudun hijirar Palasdinu da ke kasashen waje

2022-03-10 11:29:53 CRI

A jiya Laraba, ofishin kasar Sin da ke Palasdinu ya bayar da sanarwar cewa, an mika gudummawar rigakafin Covid-19 rukuni na uku da kasar Sin ta samar wa ‘yan gudun hijirar Palasdinu da ke kasashen waje ga ofishin MDD mai kula da samar da agaji ga ‘yan gudun hijirar Palasdinu, tare da kai su kasar Lebanon, wadanda za a yi amfani da su don yi wa ‘yan gudun hijirar Palasdinu da ke Lebanon rigakafin. Da haka, kasar Sin ta samar da gaba dayan gudummawar rigakafi dubu 200 ga ‘yan gudun hijirar Palasdinu da ke kasashen waje, wadanda aka kai su kasashen Jordan da Syria da ma Lebanon. (Lubabatu)