logo

HAUSA

Sin ta dauki matakan saukaka rayuwar masu bukata ta musamman

2022-03-10 11:09:09 CRI

Kasar Sin tana dora matukar muhimmanci wajen kare hakkin masu bukata ta musamman, har ma an shigar da aikin kawar da matsaloli gare su cikin shirin raya tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma na kasar. A yayin da ake aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin karo na 13, wato daga shekarar 2016 zuwa 2020, an samar da hidimar gyara gidajen kwana ga masu bukata ta musamman dubu 65 wadanda aka yi rajistarsu, sabo da tsananin nakasar da suka samu don su samu saukin rayuwa da kuma fita daga kangin talauci.

Baya ga haka, an sha aiwatar da gyare-gyare ga manyan ababen more rayuwa ta fannin zirga-zirga, don saukaka yanayin zirga-zirgarsu.

A cikin makarantu ma, an kafa na'urorin da za su taimaka wajen saukakawa dalibai masu bukata ta musamman.

Sai kuma a fannin sadarwa, kasar Sin ta yi kokarin kawar da matsalolin da tsoffafi da masu bukata ta musamman suke fuskanta wajen amfani da shafukan yanar gizo da ma sauran fasahohin zamani, don fadada kafofin sadarwa gare su, ta yadda za su ji dadin rayuwarsu ta zamani.(Lubabatu)