logo

HAUSA

Masanin Zimbabwe: Yadda kasar Sin ke bude kofarta ga ketare ya samar da damammaki ga ci gaban duniya

2022-03-10 10:59:25 CRI

Taruka biyu na kasar Sin(Taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar CPPCC) ya jawo hankalin masanan kasa da kasa. A zantawar da muka yi da masanin ilmi na kasar Zimbabwe Mongameli Dlamini a kwanan baya, ya bayyana cewa, duk da annobar Covid-19 da ke ci gaba da addabar duniya, kasar Sin ta samu nasarorin a zo a gani wajen bunkasa tattalin arzikinta, kuma yadda kasar ke bude kofarta ga kasashen ketare, ya samar da damammaki ga ci gaban duniya. Ya ce,“A yayin da tattalin arzikin duniya ke ta kara dunkulewa, kasa da kasa suna kara dogara ga juna ta fannin tattalin arziki. A ganina, bunkasuwar kasar Sin ta samar da dabara ga sauran kasashen da ke fatan farfado da tattalin arzikinsu daga illolin da annobar Covid-19 ta haifar musu. Yadda kasar Sin take sa kaimin dunkulewar bunkasuwar tattalin duniya a yanayi na daidaito da cin moriyar juna, zai amfana wa sauran kasashen duniya.”

Mongameli Dlamini ya kuma tabo batun hadin gwiwar Sin da sauran kasashe masu tasowa a fannin samar da rigakafin cutar Covid-19, inda ya ce, hakan zai gaggauta aikin yiwa al’ummar kasashe masu tasowa rigakafin, ciki har da al'ummar kasashen Afirka, inda kuma hakan zai taimaka wajen shawo kan cutar.(Lubabatu)