logo

HAUSA

Shugabar kungiyar matan jihar Xinjiang ta yi bayani kan yadda ake kare hakkin mata a jihar

2022-03-10 11:21:04 CRI

A ranar 8 ga wata, shugabar kungiyar matan jihar Xinjiang mai zaman kanta ta Uygur ta kasar Sin, Ayinuer Maihesaiti ta gabatar da jawabi, a wajen taro karo na 49 na hukumar kula da hakkin dan Adam ta MDD, inda ta yi bayani kan yadda kasar Sin ke kare hakkin matan jihar.

Ayinuer Maihesaiti ta ce, gwamnatin jihar na matukar dora muhimmanci wajen kare hakkin mata, inda ta dauki matakai na kare hakkinsu na dimokuradiyya, sai kuma hakkinsu na haihuwa, wato a yayin da ake gudanar da shirin tsara iyali, al'umma 'yan kabilu daban daban suna iya yanke shawara kan ko za su yi amfani da matakan hana daukar ciki ko a'a, da kuma irin matakin da za su dauka bisa amincewar ransu, a yayin da gwamnati ke samar da hidimomin samun haihuwa lafiya a gare su. Baya ga haka, an kuma dauki matakai na kare lafiyar mata, wadanda suka kyautata lafiyarsu a zahiri, tare kuma da daukar matakai na tabbatar da hakkin mata na samun ilmi, da guraben aikin yi, wadanda suka kai ga kara kason matan da suka samu ilmi a jami'o'i da kuma guraben aikin yi. Yanzu haka, mata sun kasance babban ginshiki wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar jihar ta Xinjiang. (Lubabatu)