logo

HAUSA

Uganda ta hau matsayi na 5 a mizanin kasuwannin hada-hadar kudi na Afrika na 2021

2022-03-10 11:05:20 CRI



Kasar Uganda ta hau matsayi na biyar yayin da ta samu maki 57 cikin kasashe 23 a binciken da aka gudanar na kasuwannin hada-hadar kudi na Afrika na shekarar 2021.

Binciken wanda kungiyar Absa Group, ta fitar ranar Laraba ya bayyana cewa, kasar Uganda ta samu dagawa daga matsayi na 10 idan an kwatanta da binciken da aka gudanar a shekarar 2020.

A cewar bankin, binciken ya yi nazari ne kan cigaban kasuwannin hada-hadar kudade ta kasashe 23, inda take zabo kasashen dake samun tagomashi a fannin ingantaccen muhallin kasuwanci.

Kasashen Ghana da Uganda, sun shiga jerin mafiya nagarta biyar a karon farko, yayin da dukkansu suka samu karin maki, kamar yadda binciken ya nuna. Kasashen Afrika ta kudu, da Mauritius da Najeriya, sun cigaba da rike kambunsu na zama a sahun gaba a bisa kididdigar, koda yake, an dan samu raguwar maki kadan na dukkan kasashen uku a shekarar 2021.

Michael Atingi-Ego, mataimakin shugaban babban bankin kasar Uganda, a yayin da yake gabatar da jawabi, a lokacin kaddamar da binciken ya bayyana cewa, duk da matsalolin da annobar COVID-19 ta haifar, amma kasar Uganda ta taka rawar gani. Ya ce alkaluman sun nuna cewa, akwai bukatar a cigaba da kiyaye kyawawan manufofi da dabarun da za su kara inganta kasuwar hada-hadar kudi don samun sauye-sauyen bunkasar tattalin arzikin kasar da zaman rayuwar alumma.(Ahmad)