logo

HAUSA

Sin ta yi maraba da matakan diflomasiyya da ake dauka domin warware rikicin Rasha da Ukraine

2022-03-10 19:25:50 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi maraba da dukkanin matakan diflomasiyya da ake dauka, domin warware rikicin Rasha da Ukraine, ciki har da taron da ministocin wajen kasashen Rasha da Ukraine da Turkiyya suka gudanar a yau Alhamis a Antalya na Turkiyya.

Zhao ya yi wannan tsokaci ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. (Saminu)